Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Saraki Ya Halarci Jana'izar Ƙanin Dangote A Kano

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya halarci jana'iz...Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya halarci jana'izar Alhaji Sani Dangote yau a Kano.

Sani Dangote ƙani ne ga attajirin nan Alhaji Aliko Dangote. 

Tun da sanyin safiyar yau Laraba ne manyan mutane daga Nijeriya da sauran sassan duniya suka yi wa Birnin Kano dafifi, inda suka tarbi gawar Alhaji Sani a babban filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Bayan tarbar gawar, Dakta Abuabakar Bukola Saraki, Dangote, Otedola, da sauran manyan mutane sun garzaya fadar mai martaba sarkin Kano, inda aka sallaci mamacin. 

Tawagar ta su Dakta Saraki ta raka gawar Alhaji Sani zuwa makwancinsa  a makabartar Dala.

Zuwa yanzu dai ana ci gaba da zaman makoki a gidan Alhaji Aliko Dangote dakeSaraki Ya Halarci Jana'izar Ƙanin Dangote A Kano

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya halarci jana'izar Alhaji Sani Dangote yau a Kano.

Sani Dangote ƙani ne ga attajirin nan Alhaji Aliko Dangote. 

Tun da sanyin safiyar yau Laraba ne manyan mutane daga Nijeriya da sauran sassan duniya suka yi wa Birnin Kano dafifi, inda suka tarbi gawar Alhaji Sani a babban filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Bayan tarbar gawar, Dakta Abuabakar Bukola Saraki, Dangote, Otedola, da sauran manyan mutane sun garzaya fadar mai martaba sarkin Kano, inda aka sallaci mamacin. 

Tawagar ta su Dakta Saraki ta raka gawar Alhaji Sani zuwa makwancinsa  a makabartar Dala.

Zuwa yanzu dai ana ci gaba da zaman amsar gaisuwa a gidan Alhaji Aliko Dangote dake Birnin Kano.

No comments