A wata ganawar da ta gudana tsakanin kungiyar ci gaban kasar Dukku da Mai Martaba Sarkin Dukku Alhaji Haruna Rashid II a shekara...
A wata ganawar da ta gudana tsakanin kungiyar ci gaban kasar Dukku da Mai Martaba Sarkin Dukku Alhaji Haruna Rashid II a shekaranjiya Lahadi 28 ga watan Nuwamban 2021 a fadarsa, Sarkin na son kowanne Hakimi ya koma garinsa ya zauna.
Umar Babagoro, Jami'in hulda da jama'a na kungiyar 'Dukku Community Progressive Association' ne ya bayyana hakan a sanarwar manema labarai da ya aiko wa da MADOGARA da safiyar yau Talata.
Sanarwar mai dauke da kwanan watan 29 ga watan Nuwamban 2021, ya bayyana cewa; kungiyar 'Dukku Community Progressive Association (DCPA)' ta bayyana wa Mai Martaba taimakon da Dr. Bello Maigari wakilin ilimin Dukku ya turo ma kungiyar, da tsarin yadda kungiyar za ta sarrafa wannan taimako.
Kungiyar ta gabatar da wasu koken jama'a a gaban Mai Martaba, tare da neman shawarwarin hanyar magance matsalolin.
Mai Martaba Alhaji Haruna Rashid II ya bayyana Dr. Bello Maigari a matsayin masoyi, kuma mai kokari akan harkokin ci gaban kasar Dukku. Sannan ya koka da irin yadda wasu masu babura suke tukin ganganci, wanda hakan yake jawo asarar rayuka, da miyagun raunuka. Mai Martaba ya kara da nuna takaicinsa bisa yadda rikicin manoma da makiyaya ya ki ci yaki cinyewa.
A wani bangaren kuma Sarkin Dukku ya bayyana sha'awarsa na komawar dukkannin Hakimai garuruwansu su zauna tare da jama'ar su, wanda hakan zai kawo karshen wasu matsaloli, kuma hakan zai iya kawo babban ci gaba a kasa baki daya.
A karshe Mai Martaba ya bayyana gamsuwarsa kan yadda kungiyar 'DCPA' take gudanar da ayyukanta, tare bada shawarwarin jajircewa wajen ganin ayyukan kungiyar ba su tsaya ba.
No comments