Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Musulmi Ya Jaddada Kudurin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Nijeriya

Daga Zubairu .Lawal  Sarkin Musulmin Nijeriya Alhaji Sa'ad Abubakar ya jaddada kudurinsa na tabbatar da zaman lafiya a taray...

Daga Zubairu .Lawal 

Sarkin Musulmin Nijeriya Alhaji Sa'ad Abubakar ya jaddada kudurinsa na tabbatar da zaman lafiya a tarayyar Nijeriya. Ya Kuma yabawa Sarakunan Gargajiya na Nijeriya saboda yadda suke bada gudumawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya.

Da yake jawabi a taron Sarakuna da masu ruwa da tsaki wanda Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tare da hadin guiwar kungiyoyin agaji masu zaman Kansu.

Taron ya hada Sarakunan Gargajiya na Arewaci da Malaman Addini da Shugabannin kungiyoyi.

Ya ce; Sarakuna suna kusa da jama'a kuma suna lura da yadda al'ummomi ke gudanar da ayyukan zamantakewa a tsakaninsu.

Bilhasali Sarakunan Gargajiya na sanya ido da duba rayuwar jama'a da tattauna lamurar zaman takewa da bai wa jama'a shawarwari na zaman lafiya da hadin kai a tsakaninsu.

Sannan ya yi kira ga gwamnatoci da su rika hadin kai da Sarakuna wajen tabbatar da ci gaban al'umma domin karfafa zaman lafiya.

Shima Shugaban Kungiyar Kiristocin Nijeriya Rabaran Samson Ayokunle, ya yaba da kalaman Sarkin Musulmai na cewa ya kamata al'umman Nijeriya su zama tsintsiya madaurinki guda, su kuma fahimci juna su zauna lafiya.

A jawabinta Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad ta yi kira ga Gwamnatoci da Sarakunan Gargajiya da su rika daukar mataki na yaki da cin zarafin mata da yara kanana.

Ta ce; ya kamata a daina tura yara kanana aikin aikatau saboda yana janyo damuwa wasu yaran ta nan ne suke fadawa halin kunci.

Ministan Harkokin Mata Misis Dame Pauline Tallen, ta yabawa Sarakunan Gargajiya kan yadda suka taka rawa wajen fadakar da al'umma mahimmanci kiwon lafiya a lokacin Korona.

Ta roke su da su ci gaba da bai wa yaki da cin zarafin mata da yara kanana goyon baya.

No comments