Rahotanni sun bayyana cewa Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta sake shigar da ƙara inda ta nemi kotu ...
Rahotanni sun bayyana cewa Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta sake shigar da ƙara inda ta nemi kotu ta hana wa shugaba Buharikashe naira biliyan 26 da aka ware masa na tafiye tafiye da abinci da kula da harakokin ofishinsa.
Majiyarmu ta labarto cewa SERAP ta ce ta shigar da Æ™arar ne a babbar kotun Abuja a ranar Juma’a, tana mai cewa “bai dace da buÆ™atun al’umma ba a fifita tafiye tafiye da abinci yayin da kuma aka ware naira biliyan 19.17 kawai don ayyukan asibitocin koyarwa guda 14.”
“KuÉ—irin kashe naira biliyan 26 rashin adalci ne ga talakawan Najeriya kuma wani nauyi ne ga masu tasowa,” in ji SERAP.
SERAP ta sha kai gwamnatin Najeriya Æ™ara kan batutuwa da dama amma har yanzu babu shari’a É—aya da aka yanke.
No comments