Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shan Barasa Ya Kashe Mutum 35 A Indiya

'Yan sandan sun kama mutane 19 an kuma dakatar da wasu jami'an tsaro 9 bayan samun mutuwar mutane da dama da suka sha ba...


'Yan sandan sun kama mutane 19 an kuma dakatar da wasu jami'an tsaro 9 bayan samun mutuwar mutane da dama da suka sha barasa a wasu mashaya guda uku a wata gunduma da ke jihar Bihar.

Yanzuz haka dai 'yan sanda sun kaddamar da bincike, har ma an kama mutane 19 da ake zargi da hannu a lamarin, an kuma dakatar da 'yan sanda 9 daga aiki.

Hukumomin a Indiya ta ce akalla mutane 1,000 na mutuwa duk shekara yawanci daga yankuna marasa galihu sakamakon shan barasar gargajiya. Ko a shekarar 1992 mutane 200 sun mutu a jiyahar Odisha da ke gabashin Indiya wasu 180 sun mace a yammacin Bengal a 2011.

Dama dai gwamnatin jihar da lamarin ya faru ta haramta sha da sayer da barasa gabannin zabukan kananna hukumomi da aka gudanar a 2016.


No comments