An buga kunnen doki tsakanin Nijeriya da Cape Verde a yayin da aka tashi wasa daya da daya a fafatawar da suka yi ta neman samun...
An buga kunnen doki tsakanin Nijeriya da Cape Verde a yayin da aka tashi wasa daya da daya a fafatawar da suka yi ta neman samun tikitin shiga Gasar Kofin Duniya.
Victor Osimhen ne ya ci wa tawagar Super Eagles kwallo a minti daya da fara wasa, sai dan wasan Cape Verde Stopira ya farke a minti 6 a karawar da ta gudana ranar Talata a filin wasa na Teslim Balogun da ke birnin Ikko.
A yanzu dai Nijeriya ce ke kan gaba a rukunin C da maki 13 bayan wasa 6.
Nijeriya ta ci wasa hudu ta yi kunnen doki daya, sannan aka doke ta a wasa daya.
Cape Verde ke biye mata da maki 11, wadda ta ci wasan uku, kunnen doki biyu sannan aka doke ta a daya.
Da wannan sakamakon, yanzu Nijeriya za ta fafata wasan fidda gwani (play-off) domin samun shiga Gasar Kofin Duniya.
No comments