Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya kai ziyara garin Banibangou yankin Tillaberi domin jajantawa al’ummar yankin kamar yadda BBC ta labarto.
A ranar Alhamis gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana biyu domin jimamin kashe mutum 69 a harin da mayaƙa masu iƙirarin jihadi suka kai a Banibangou da ke kusa da kan iyaka da Mali.
Bazoum ya ce ziyara ce da ta zama dole gare shi bisa abin da ya faru.
"Aiki na ne a lokaci irin wannan na zo da kaina na taya ku jaje,” kamar yadda shugaban ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Shugaban ya ce ya kai ziyarar ne a madadin al’ummar Nijar tare da yi wa al’ummar yankin alÆ™awalin cewa gwamnati za ta yi Æ™oÆ™arin gano bakin zaren magance matsalolin tsaro a yankunan da ke kan iyaka.
Yankin da ke kan iyaka da Nijar da Mali da Burkina Faso ya sha fuskantar hare-hare daga mayaƙan da ke da alaƙa da ƙungiyoyin IS da kumna Al Qaeda.
0 Comments