Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Malam Mamman Daura Murnar cikarsa Shekaru 82 da haihuwa a ranar 10 ga watan Nuwamba. Shugaban ya ...
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya
taya Malam Mamman Daura Murnar cikarsa Shekaru 82 da haihuwa a ranar 10 ga
watan Nuwamba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wata
sanarwa da Kakakinsa, Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu.
Shugaba Buhari ya ce babu wanda yafi
dacewa da ya taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa kamar Malam Mamman
Daura, inda ya bayyana shi a matsayin "Mutum mai cikar nagarta wanda da
dama ake mutuntawa kan yadda ya nemi ilmi kuma yake da cikaƙƙiyar hankali da sanin
yakamata sa'annan ya yi fice wurin Æ™afewa kan aikata daidai”, inji shugaban.
“Allah ya Albarkace ka da koshin
lafiya da jindadi domin ci gaba da aiki wa kasa. Ka ci gaba da kasancewa cikin
halin lafiya domin yawaita aiki wa kasa, Allah ya Albarkace ka da tsawon rayuwa
cikin koshin lafiya”, inji sanarwar.
No comments