Gwamantin Habasha ta ce Firaministan kasar Abiy Ahmed, ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Demeke Mekonnen Hassen, inda ya wuc...
Gwamantin Habasha ta ce Firaministan kasar Abiy Ahmed, ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Demeke Mekonnen Hassen, inda ya wuce fagen daga wajen jagorancin sojoji a daidai lokacin da ‘yan tawaye ke ci gaba da mamaye yankunan kasar.
Mai magana da yawun gwamnatin Habasha Legesse Tulu, ya ce tuni firaministan ya danka ragamar tafiyar da ayyukan gwamnati a hannun mataimakinsa Demeke Mekonnen Hassen kamar dai yadda wata kafar yada labaran kasar mai suna Fana ta ruwaito.
Tun a ranar Litinin da ta gabata ne Abiy ya sanar da aniyarsa ta jagorantar dakarun kasar zuwa fagen daga domin datse ‘yan tawayen Tigray da ke ci gaba da mamaye yankunan kasar, yayin da ‘yan tawayen da kuma kawayensu ke cewa za su iya kwace birnin Adis Ababa a cikin gajeren lokaci.
To sai dai bayanai sun ce yanzu haka mazauna birnin na Adis Ababa sun fara gudanar da sintiri don kare birnin daga duk wata barazanar kai masa hari duk da cewa sun ce suna fuskantar karancin makamai don tafiyar da wannan aiki.
Tuni dai Amurka ta bayyana wannan rikici a matsayin wanda zai iya kawo wa tattalin arzikin kasar ta Habasha mummunan koma-baya.
No comments