Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojin Kamaru Sun Kashe Kwamanda Da Mayakan 'Yan Aware 7 A Bamenda

  Dakarun Sojin Kamaru sun sanar da kisan guda cikin kwamandojin ‘yan awaren kasar da ke kaddamar da hare-hare a yankunan da ke amfani da tu...

 


Dakarun Sojin Kamaru sun sanar da kisan guda cikin kwamandojin ‘yan awaren kasar da ke kaddamar da hare-hare a yankunan da ke amfani da turancin Ingilishi, yayin wani sumame kan mayakan a karshen mako.

Majiyoyin tsaro a Kamaru sun ce an hallaka fitaccen kwamandan na ‘yan aware ne da ake kira da Janar Cross and Die a tsakanin ranakun 29 ko kuma 30 ga watan da ya gabata na Oktoba, yayin sumame a yankin Ntamafe da ke Mankon a birnin Bamenda.

Sanarwar rundunar Sojin Kamaru ta ce kwamanda Cross and Die na cikin mayaka 8 da dakarunta suka hallaka amma ba tare da bayyana takamaiman ranar da lamarin ya faru ba.

Kwamandan runduna ta 5 ta hadakar Sojin Kamaru Birgediya Janar Nka Valere ya ce dakarunsu sun shammaci janar cross and die ne lokacin da yak e halartar jana’izar wani dan uwansa a Ntamafe ranar juma’ar da ta gabata inda suka hallaka tare da mayakan ‘yan awaren 7.

Tuni dai mataimakin babban kwamandan dakarun ‘yan awaren Janar Capo Daniel ya tabbatar da kisan na janar cross and die cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa ranar asabar.

Babu dai cikakken bayani kan yadda kisan babban kwamandan na ‘yan awaren Kamarun ya faru bayan da dakarun sojin kasar suka ki yiwa manema labarai karin bayani, sai dai faifan bidiyon da Janar Capo Daniel ya wallafa ya yi ikirarin cewa sojojin kasar sun bi sahun motar kwamandan tare da bude masa wuta wanda ya shafi tarin fararen hula.

Sanarwar da Janar Capo Daniel ya wallafa ya ce tuni suka nada magajin Janar cross and die don ci gaba da jan ragamar ayyukansa a sansanin ‘yan awaren na Ntankah da suke kira da sabuwar Jerusalem.


-Rfi

No comments