Ayarin motocin sojojin Faransa da ke kan hanyarsu ta zuwa kasar Mali sun bude wa masu zanga-zangar lumana wuta a garin Tera da k...
Ayarin motocin sojojin Faransa da ke kan hanyarsu ta zuwa kasar Mali sun bude wa masu zanga-zangar lumana wuta a garin Tera da ke jamhuriyar Nijar bayan shafe sama da mako guda fararen hular na gudanar da zanga-zangar lumana kan kin amincewa da shigo da dakarun sojojin Faransar a Burkina Faso.
Ayarin motocin sojin na Faransa da suka sauka a kasar Ivory Coast cikin makon jiya, sun fara tsallakawa ne Burkina Faso, kuma a ranar Juma'a suka shiga Nijar a kan hanyarsu ta zuwa tsakiyar Mali, inda masu zanga-zangar lumana a garin Tera dake yammacin kasar ta Nijar suka gudanar da zanga-zangar lumanar hana dakarun wucewa.
Sojojin na Faransa sun kashe fararen hula uku da jikkatar mutum 18 a jiya Asabar.
Tawagar dakarun na Faransa dai na kan hanyarsu ta zuwa sansaninsu a garin Gao dake Mali, inda suka yi hedikwatar din-din-din ta rundunar Barkhane.
Yayin karin bayani kan halin da ake ciki, Kakakin sojojin Faransa Pascal Ianni ya ce Babu wani sojansu da ya samu rauni.
No comments