Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Soludo Na APGA Ya Lashe Zaben Gwamnan Anambra

  Hukumar zaben Nijeriya wato INEC ta bayyana dan takarar jam'iyyar APGA Charles Chukwuma Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan...

 Hukumar zaben Nijeriya wato INEC ta bayyana dan takarar jam'iyyar APGA Charles Chukwuma Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar.

Soludo wanda jam'iyyarsa ta APGA ta shugabanci jihar na tsawon shekaru 16 ya sami nasara da gagarumar ratar kuri'u fiye da dubu daya kan abokin hamayyarsa na jam'iyya mai mulki ta APC Andy Uba.

Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Soludo murna, tare da bukatarsa da ya magance kalubalen da jiharsa da kuma yankin ke fuskanta.

Fiye da 'yan sanda dubu 30 ne dai aka tura jihar da ke zama guda daga cikin yankin da 'yan kungiyar IPOB ke rajin ballewa don kafa kasar Biafra. Da dama na ganin Soludo ka iya fuskantar kalubalen daga abokan hamayyarsa.

No comments