Isra’ila ta nuna sha’awarta na nuna goyon bayanta ga wasu ‘yan takara guda biyu da suke neman shugabancin kasar Libya a zaben da za’a yi a...
Isra’ila
ta nuna sha’awarta na nuna goyon bayanta ga wasu ‘yan takara guda biyu da suke
neman shugabancin kasar Libya a zaben da za’a yi a watan gobe , da nufin share
hanyar kulla hulda tsakaninta da gwamnati mai zuwa,
Jaridar
Al-akhbar Daily ta kasar Lebanon ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa
gwamnatin Yahudawan sahayoniya ta nuna gamsuwa da wasu ‘yan takarar shugabancin
kasar ta Libya da suka hada da Janaral Khalifa Haftar da kuma Saifil Islam
Ghaddafi dan tsohon shugaban gwamnatin kasar da aka kashe, a matsayin wadanda
za su iya cika mata burinta na kokarin sake kulla huldar Diflomasiya da kasar.
Rahoton
ya jaddada cewa ‘yan takarar shugabancin kasar guda biyu a shirye suke su
daidaita alakarsu da Isra’ila kuma zai kasance wani bangare ne daga cikin
shirye-shiryen da suke yi da ba a bayyana ba, domin gudun ka da lamarin ya
shafi kuri’un da za su samu a lokacin zabe, musamman idan aka yi la’akari da
yadda al’ummar Libya suke adawa da kulla hulda da Isra’ila kamar yadda rahoton
Al-akhbar ya ce.
Wannan
yana zuwa ne bayan ziyarar da babban dan Janar Khalifa Haftar ya kai Isra’ila a
watan jiya, inda ya gana da jami’an gwamnatin Isra’ila kuma ya nuna gamsuwarsa
da batun kulla hulda tsakanin Tel aviv da kuma Tripoli , ita kuma ta yi
alwashin bawa Libya duk wani taimakon soji da na siyasa idan har aka daidaita
alaka tsakani .
No comments