Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tambuwal Ya Ɗau Nauyin Karatun Ɗaliban Sakkwato 100 A Jami'ar Al-Istiqama Kano

Gwamnatin Jihar Sakkwato, ƙarƙashin jagorancin Gwamna  Aminu Waziri Tambuwal, ta ɗauki nauyin ɗalibai ƴan asalin jihar guda 100 ...


Gwamnatin Jihar Sakkwato, ƙarƙashin jagorancin Gwamna  Aminu Waziri Tambuwal, ta ɗauki nauyin ɗalibai ƴan asalin jihar guda 100 domin su yi karatun digiri a jami'ar Al-Istiqama da ke Jihar Kano.

Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta Jihar Sakkwato, Altine Shehu Kajiji, shi ne ya gabatar da ɗaliban ga jami'ar ta Al-Istiqama da ke Ƙaramar Hukumar Sumaila a jihar Kano.

Da yake gabatar da ɗaliban, Kajiji ya baiyana cewa a yanzu ya kawo rukunin farko na dalibai 37 ne a cikin guda 100 ɗin da gwamnatin jihar zata kawo a jami'ar. 

Da ya ke karɓar ɗaliban a madadin shugaban jami'ar, Dr Kabiru Muhammad Kofa ya baiyana cewar jami'ar Al-Istiqama ta dace da karantarwar kowane irin zamani, inda ya ƙara da cewa jami'ar za ta kula da karatu, tarbiyya da kuma tabbatar da cewar ɗalibai na kiyaye dokokin jami'ar.

Haka kuma, Kofa ya yabawa gwamnatin jihar Sokoto a kan ƙoƙarin na baiwa ƴan jihar tallafin karatu domin bunƙasa harkar ilimi a jihar.

-Daily Nigerian

No comments