Tinubu Na So Na Goyi Bayansa Ya Shugabanci Nijeriya - Tanko Yakasai


Ɗaya daga cikin dattawan arewacin Nijeriya Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa zai goyi bayan tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu a yunƙurin da Tinubun yake na neman shugabancin Nijeriya.

A wata hira da jaridar Punch, Tanko Yakasai ya shaida cewa Tinubu ya zo wajensa ne a ranar Laraba domin ya nemi goyon bayansa.

Duk da cewa Tinubu bai fito fili ya bayyana cewa zai yi takarar shugabancin ƙasa ba, amma akwai rahotanni da dama da ake yaɗawa cewa zai tsaya takarar.

Haka ma akwai hotuna da kuma manyan allunan kan hanya ɗauke da hoton Tinubu a wasu sassa na Nijeriya da ke nuna alamun zai tsaya takarar shugabancin Nijeriya kamar yadda BBC suka ruwaito. 

Post a Comment

0 Comments