Daruruwan tsoffin ‘yan kungiyar Boko Haram da suka tuba suka gabatar da kansu ga dakarun Nijeriya sun yi zanga-zanga a sansanin da aka aji...
Daruruwan
tsoffin ‘yan kungiyar Boko Haram da suka tuba suka gabatar da kansu ga dakarun Nijeriya
sun yi zanga-zanga a sansanin da aka ajiye su da ke kusa da Maiduguri a jihar
Borno.
Tsoffin
mayakan kungiyar ta Boko Haram na bukatar a ba su damar yanka shanu domin samun
nama da za su ci.
Sun
yi boren ne dauke da makamai da suka hada da adduna, gatari da sanduna suna
barazanar kashe duk wanda ya fice daga sansanin da aka jibge su a lokacin
boren.
Wannan
na nuna irin gagarumin aikin da Hukumomin kasar ke yi domin sauya ra'ayoyin
tsoffin mayakan kungiyar ta Boko Haram domin su iya zama cikin al’umma bayan da
aka kwashe shekaru 12 ana fafata yaki da su.
Kimanin
tsoffin mayakan kungiyar Boko Haram 250
da suka hada da maza da mata da kananan yara, wadanda aka tsugunar a Unguwar Gidan
Taki dake bayan garin Maiduguri suka shiga boren.
Majiyoyin
samun labarai na cewa yayin boren
tsoffin mayakan kungiyar Boko Haram sun farfasa taga da kofofin gidajen da ke sansanin
da aka ajiye su kamar yadda RFI ta labarto.
No comments