Daga Ammar Muhammad Rajab Adil Al-Kalbani, tsohon limamin ka'aba, ya gabatar da takaitaccen bayani kan matsayinsa a cikin w...
Daga Ammar Muhammad Rajab
Adil Al-Kalbani, tsohon limamin ka'aba, ya gabatar da takaitaccen bayani kan matsayinsa a cikin wani shirin fim na bidiyo na minti 2 da dakika 41.
Yankin Riyadh Kashi na 2021 mai suna 'Combat Field' za a gabatar da shi a cikin wani fim na talla wanda ya hada da tsohon Imam Kaaba Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani da wasu taurarin kwallon kafa.
Baya ga tada kura a shafukan sada zumunta, masu amfani da shafukan na ci gaba da yi wa tsohon Limanin Ka’aba din tofin Allah ya tsine da fatan Allah ya shirya shi.
Sheikh Adil Al-Kabbani ya bayyana ne a cikin wani faifan bidiyo na talla wanda ke nuna yadda sojoji ke yaki da kuma sarrafa makaman yakin. Tsohon Limamin Ka'aban ya yi takaitaccen bayani a cikin faifan bidiyon, wanda ya dauki tsawon mintuna 2 da dakika 41.
Shugaban Hukumar lura da nishadi ta Saudiyya, Turk al-Sheikh ya sanya faifan bidiyon a shafinsa na Twitter, inda tsohon Limamin Kaaba din, Adil al-Kalbani cikin barkwanci ya rubuta cewa; “kuna tunanin zan iya zuwa Hollywood?”
Sai dai masu amfani da shafukan sada zumunta din sun caccaki Sheikh Adil Al-Kalbani bayan fitowarsa a faifan bidiyon na tallar. A Lokacin da wani mai amfani da shafukan sada zumunta ya rubuta cewa kasancewar ku a cikin bidiyon baƙon abu ne, sai wani mutum ya amsa masa da cewa, "Allah ya yi muku jagora ya buɗe zuciyar ku."
No comments