Tsohon Manajan Daily Trust, Abdulrahman Huseini Ya Rasu


Daga Ammar M. Rajab

Allah ya yi wa Malam Abdulrahman Huseini rasuwa. Malam Husaini tsohon Manajan Kamfanin Jaridar Daily Trust ne. 

Abdulrahman Huseini ya rike mukamin Manajan ci gaban kasuwanci da tsare-tsaren taruka na Daily Trust. 

Majiyarmu ta Daily Trust ta labarto cewa; ya rasu a Abuja a yau Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya. 

Kafin rasuwarsa, Marigayin shi ne mawallafin Mujallar Inclusion Magazine wacce take maida hankali wajen kawo rahotanni kan mutanen dake da lalura (PLWDs). 

Marigayin memba ne a majalisar Masarautar Bida, inda yake rike da sarautar Sarkin Arewan Nupe. 

Tuni aka bizne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a mahaifarsa ta Bida dake jihar Neja.

Post a Comment

0 Comments