Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Ya Yi Nasara A Kotu Kan Ganduje

Wata kotu a birnin Tarayya Abuja ta yanke hukuncin cewar dauke tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II daga Kano zuwa Nasarawa...


Wata kotu a birnin Tarayya Abuja ta yanke hukuncin cewar dauke tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II daga Kano zuwa Nasarawa bayan tube shi daga karagar mulki a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2020 ya saba ka’ida.

Alkalin kotun Anwuli Chikere yayin yanke hukuncin ya ce dokar Majalisar Masarautar ta shekarar 2019 da gwamnatin Jihar Kano ta yi amfani da ita wajen kai Sarki Sanusi Jihar Nasarawa ya sabawa kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.

Chikere ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya fi karfin duk wata doka da aka yi, saboda haka tsohon Sarkin na da hurumin zama inda yake so a Nijeriya ciki harda jihar Kano kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi dama.

Kotun ta bai wa gwamnatin jihar Kano da Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya da Darakta Janar na Hukumar DSS umurnin biyan diyyar naira miliyan 10 da kuma neman gafarar tsohon Sarkin a cikin manyan jaridun kasar guda 2.

Sarki Sanusi ya shigar da karar ne inda ya bukaci kotu da ta haramta tsare shi da aka yi wanda ya sabawa 'yancinsa da kuma dauke shi daga Kano.

Wannan ya biyo bayan sauke shi daga karagar mulki a matsayin Sarkin Kano na 14 da gwamnatin jihar Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta yi, inda ta maye gurbinsa da Sarki Aminu Ado Bayero.

Sarki Sanusi bai kalubalanci sauke shi daga karagar mulki da gwamnatin jihar Kano ta yi a gaban kotun ba, kuma ita ma kotun ba ta ce komai akan raba shi da sarautar ba.

No comments