Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Yi Bayanin Yadda Za A Hada Kan 'Yan Nijeriya

Tsohon shugaban Ni jeriya Dr Goodluck Jonathan ya bada shawarar hanyoyin da ya dace a bi wajen samun dunkulalliyar kasa mai cike...


Tsohon shugaban Nijeriya Dr Goodluck Jonathan ya bada shawarar hanyoyin da ya dace a bi wajen samun dunkulalliyar kasa mai cike da zaman lafiya.

Jonathan wanda ya bayyana cewar Allah Ya wadata Nijeriya da arzikin jama’a da kuma albarkatu daban daban, ya kara da cewar za a ci gajiyar su ne kawai idan an samu dawwamammen zaman lafiya a cikin kasar kamar yadda Rfi ta labarto.

Tsohon shugaban ya bukaci shugabanni da su mayar da hankali wajen gina hadin kan kasa da yin adalci ga kowanne bangare ba tare da fifita wata kabila ko jama’a akan wata ba.

Jonathan ya ce babban kalubalen dake gaban shugabanni shi ne hada kan jama’ar kasa, kuma hakan ba zai samu ba muddin ana fifita wata al’umma ko kabila akan wata ba.

Tsohon shugaban ya ce muddin aka fifita wata kabila ko al’umma akan wata, za a  samu rashin hadin kai da kuma korafe korafe daga wadanda aka hana su hakkokin su na ‘Yan kasa.

Kalaman tsohon shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kabilu da yankunan Nijeriya ke korafi akan nuna musu bambanci da kuma hana su mukaman da suka ce ya dace a basu.

Daga cikin masu korafin akwai ‘Yan kabilar Igbo dake kudu maso gabashin kasar wadanda ke cewa an hana su rike daya daga cikin manyan ofisoshin tsaron kasar, a matsayin daya daga cikin korafin da masu fafutukar kafa kasar Bifra ke amfani da shi wajen bayyana dalilin yunkurin da suke na samun kasa ta kan su.

No comments