Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

UNICEF Ta Ce 'Yan Nijeriya Miliyan 46 Ke Bayan Gida A Bainar Jama'a

Hukumar UNICEF ta bayyana Nijeriya a matsayin kasar da aka fi samun yawan mutanen dake bayan gida a bainar jama’a wadanda adadin...


Hukumar UNICEF ta bayyana Nijeriya a matsayin kasar da aka fi samun yawan mutanen dake bayan gida a bainar jama’a wadanda adadin su a cewar UNICEF ya kai mutum miliyan 46.

Jami’in hukumar Sam Adejo Okedi ya ce duk da ci gaban da aka samu ‘Yan Nijeriya miliyan 46 ke bayan gida a fili, matakin dake barazana ga lafiyar jama’a a sassan kasar.

Alkaluman hukumar da aka gabatar na kananan hukumomin Nijeriya 774 sun nuna cewar a kananan hukumomi 10 ne kacal ba a samun masu bayan gida a fili, wanda shi ne kashi 10 bisa 100 a Nijeriya.

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewar an yi nasarar magance matsalar da ake samu na yawaitar masu bayan gari a bainar jama’ar a Jihohin Jigawa da Katsina da kuma Binuwe.

Shugaban hukumar UNICEF dake kula da shiyyar Kano da Sakkwato, Maulid Warfa ya bayyana haka, inda ya danganta ci gaban da matakin da hukumomin yankunan ke dauka na magance matsalar.

Warfa ya ce an samu nasarar dakile wannan dabi’ar ce a kananan hukumomi 21 dake Katsina da 18 dake Jigawa da kuma guda 9 dake Binuwe.

Jami’in ya ce kashi 25 na mutanen dake zama a yankin arewa maso yammacin Nijeriya na amfani da bayan gida wajen biyan bukatun su, yayin da kashi 35 kuma ke samun kula ta fannin tsafta.

No comments