Daga Muhammad Farouk Yara mata guda bakwai wanda ya hada da ƴan shakara 10 zuwa 12 suka rasa rayukansu a wani haɗarin kwale-kwal...
Daga Muhammad Farouk
Yara mata guda bakwai wanda ya hada da ƴan shakara 10 zuwa 12 suka rasa rayukansu a wani haɗarin kwale-kwale wanda ya kife da su a kan hanyarsu ta zuwa bikin maulidi a ƙauyen Gamafoi dake Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa ta Jihar Jigawa.
Majiyarmu ta Jaridar Nation ta labarto cewa ƴan matan su 10 ne su ke tafiya daga ƙauyen Gafasa zuwa Gasanya a karamar hukumar Auyo domin zuwa wajen maulidi a daidai lokacin da ibtila'in ya faru.
Dagacin Gamafoi, Haruna Gamafoi ne ya kai rahoton haɗarin zuww ga ƴan sanda kamar yadda bayanai suka tabbatar.
Ya ce haɗarin ya faru ne wajen ƙarfe 3:30 na yamma a lokacin da jirgin ya kife da ƴan mata goma amma an yi nasara tserar da uku daga ciki, inda bakwai su ka ce ga garinku nan.
An labarto cewa ƴan matan suna sauri za su tafi garin ne kuma da suka zo gaɓar kogin Gasanya amma ba su samu mai fito ba shi ne su ka tuƙa kwale-kwalen da kan su.
Bayan haɗarin ya afku sai a ka garzaya da su asibitin Kafin Hausa inda likitoci su ka tabbatar da rasuwar 7 da ga cikinsu.
Rundunar Ƴan sanda ta Jigawa ta tabbatar da faruwar haɗarin ya zuwa hada rahoton nan.
No comments