Yajin Aikin ASUU: Majalisa Ta Shiga TsakaniMajalisar wakilai ta umarci kwamitin harkokin ilimi da ya binciki barazanar yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'in suka yi, tare da gabatar da rahoto ga majalisar.

A ranar Litinin ne kungiyar malaman ta bai wa gwamnati wa’adi kan ta mutunta yarjejeniyar da suka kulla ko kuma su shiga yajin aiki.

Wasu 'yan majalisa a zaman na yau sun bukaci a yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar duk wasu matakan da suka dace, don bude wata tattaunawa ta gaskiya da ASUU domin kaucewa shiga yajin aiki.

A cewar shugaban kwamitin harkokin ilimi mai zurfi na majalisar Honorabul Aminu Sulaiman Goro, tuni sun aike wa bangarorin biyu takardar neman shiga tsakani domin kawo karshen tirka-tirkar da ta dade tana faruwa tsakaninsu.

Kungiyar ASUU ta sha daukar matakin zuwa yajin aiki, a duk lokacin da suka samu rashin jituwa da gwamnatin Nijeriya, wanda hakan na haifar da tsaiko ga karatun daliban jami'o'i a kasar.

Post a Comment

0 Comments