Daga Fatima Idris Zariya Da yammacin ranar Laraba gungun 'yan Bindiga suka farwa kauyaku a yankin Fatika na karamar hukumar ...
Daga Fatima Idris Zariya
Da yammacin ranar Laraba gungun 'yan Bindiga suka farwa kauyaku a yankin Fatika na karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Wakiliyarmu ta zanta da wani ganau ta wayar salula kuma ya bayyana mata abubuwan da suka faru a lokacin da suka farmaki kauyakun.
Ya ce a jiya Laraba 24 ga watan Nuwamban 2021 da yamma ne misalin karfe 4 na yamma 'yan bindigar suka kunno kai a yankin take suka fara ruwan wuta ga duk wanda suka gamu da shi, a cewarsa ya zuwa yanzu ba a san addadin jama'ar da suka kashe ba.
Har wala yau 'yan bindigar sun rutsa kauyaku kamar Idasu da Rufaiya duk a karamar hukumar Giwa.
Ya zuwa yanzu dai ana radedadin cewa ba a ga daya daga cikin Sarakunan yankin ba a daidai lokacin da wasu suka fantsama daji ba a gansu ba har zuwa washe garin yau Alhamis.
Bisa haka wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin daya daga cikin mazauna yankin da lamarin ya shafa inda ya nemi a sakaya sunanasa, ya bayyana cewa; "Don Allah don Annabi gwamnati ta kara kaimi akan lamarin tsaro a jihar kaduna musamman karamar hukumar Giwa."
Tabbas bincike ya tabbatar da cewa karamar hukumar Giwa tana cikin tsaka mai wuya bisa ga yadda karamar hukumar ta yi iyaka da jihar Katsina da jihar Zamfara da jihar Neja.
Kuma duk da kokarin da gwammatin jihar Kaduna ke yi lailai jama'ar yankin na cikin wani hali kuma suna bukatar taimako.
Yanzu haka an ce tulin gawa na can ana shirin gudanar da jana'izar wanda suka riga mu gidan gaskiya a harin kamar yadda ganau ya tabbatar mana.
Wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin hukumar tsaron jihar domin jin ko wani mataki za su dauka akan lamarin. Sai dai ya zuwa hada rahoton nan ba mu samu Kakakin rundunar'yan sandan jihar Kaduna a waya ba.
Haka zalika wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar ta Giwa amma shima wayar shi ta ki shiga.
Ya zuwa hada wannan rahoton gaba daya jama'ar karamar hukumar na cikin zullumi bisa halin da ake ciki a yanzu.
Amma Malamai da Sarakuna sun nemi jama'a su ci gaba da addu'ar Allah ya kawo saukin lamarin.
Karamar Hukumar Giwa na daya daga cikin kananan Hukumomin da aka katse sadarwa a yankin a jihar ta Kaduna.
No comments