Daga Fatima Idris Zariya Da yammacin ranar Larabar makon da ya gabata ne gungun 'yan Bindiga suka farwa kauyaku a yankin Fat...
Daga Fatima Idris Zariya
Da yammacin ranar Larabar makon da ya gabata ne gungun 'yan Bindiga suka farwa kauyaku a yankin Fatika na karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
'Yan bidigar sun kashe Sarkin garin Rufayya Alhaji Muntari Rilwan da wasu mutane 8 a garuruwan dake makwabtaka da juna duk a yankin Fatika a cikin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Wakiliyarmu ta zanta da wani ganau ta wayar salula kuma ya bayyana mata abubuwan da suka faru a lokacin da barayin suka farmakin kauyakun.
Ya ce a ranar Larabar 24 ga watan Nuwamban 2021 da yamma ne misalin karfe 4 na yamma 'yan bindigar suka kunno kai a yankin Fatika take suka fara ruwan wuta ga duk wanda suka gamu da shi musamman jama'ar dake gona domin kawar da amfaninsu.
Daga cikin wanda suka dauke a wannan harin sun hada har da Sarkin garin Rufayya wanda daga bisani an tsinci gawarsa a cikin wata ciyawa sun jefar.
Bayan Sarkin akwai mutane daga kauyakun da suke kusa da juna suma an sami gawarsu bayan kurar ta lafa.
Har wala yau 'yan bindigar sun rutsa kauyaku kamar Idasu da Rufaiya duk a karamar hukumar Giwa.
Ya zuwa yanzu mazauna yankin sun kasance abin tausayawa matuka kamar yadda bincike ya nuna.
Wani abin ban tausayi shi ne yadda suka hana duk wani mai gida zuwa gona a halin yanzu duk da lokaci ne na cire amfanin gonar .
Bisa haka wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin daya daga cikin mazauna yankin da lamarin ya shafa da ya nemi a sakaya sunanasa. Ya ce; "Don Allah don Annabi gwamnati ta kara kaimi akan lamarin tsaro a jihar Kaduna musamman karamar hukumar Giwa"
Kuma ya ce yanzu haka 'yan bindigar sun raba madafan iko a karamar hukumar ta Giwa. Kuma sun sanya dokoki da suke bukata ga jama'ar yankin tare da gargadi mai zafi akan wanda duk ya sabawa dokarsu to take za su zo har gida su dauki mutum su kashe shi.
Tabbas bincike ya tabbatar da cewa karamar hukumar Giwa tana cikin tsaka mai wuya bisa ga yadda karamar hukumar ta yi iyaka da jihar Katsina da jihar Zamfara da jihar Neja.
Kuma duk da kokarin da gwammatin jihar Kaduna ta ke yi lailai jama'ar yankin na cikin wani hali kuma suna bukatar taimako.
Wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin hukumar tsaro jihar don jin ko wani mataki za su dauka akan lamarin amma abin ya ci tura. Bisa ga yadda lamarin ya yi karfi a yankin domin a fadin jihar Kaduna a yanzu babu karamar hukumar dake fama da matsalar tsaro kamar karamar hukumar Giwa.
Bincike ya nuna cewa yanzu haka babu wani mai kudi da yake zaune a gidansa a fadin kauyakun dake karamar hukumar Giwa duk sun yi hijira zuwa wasu garuruwan ba da son hakan ba.
Haka zalika wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar na Giwa amma shima wayar shi ta ki shiga saboda matsalar sadarwa a yankin.
Ya zuwa hada wannan rahoton gaba daya jama'ar karamar hukumar Giwa na cikin zullumi bisa halin da ake ciki a yanzu.
Amma Malamai da Sarakuna sun nemi jama'a su ci gaba da addu'ar Allah ya kawo saukin lamarin.
A gefe guda kuma sun nemi a karawa tsarin tsaro karfi a yanki domin lokuta da yawa ko an sanar da jami'an tsaron zuwansu na daukan lokaci wanda hakan yasa barayin dajin sukan ci karansu babu babbaka.
No comments