Marigayi Sagir Hamidu Daga Ammar Muhammad Rajab Tsohon dan takarar gwamna a zaben 2019 a jihar Zamfara, Sagi...
Marigayi Sagir Hamidu
Daga Ammar Muhammad Rajab
Tsohon dan takarar gwamna a zaben 2019 a jihar Zamfara, Sagir Hamidu, ya gamu da ajalinsa bayan da 'yan bindiga suka bude masa wuta a babban titin Abuja zuwa Kaduna.
Marigayin dan siyasar ya nemi takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
An harbe shi ne bayan da maharan suka bude wuta akan matafiya a daidai garin Rijana dake babban titin Abuja zuwa Kaduna da misalin karfe 4 na yammancin yau Lahadi.
Majiyarmu ta tsaro wacce ta nemi a sakaya sunanta kamar yadda Daily Nigerian ta labarto ya tabbatar da mutuwar tsohon dan takarar, inda ya ce; "yana daya daga cikin wadanda harsashin 'yan bindigar ya sama".
Majiyar tamu ta kara da cewa; fasinjoji da yawa da suka yi yunkurin gudu 'yan bindigar sun bude musu wuta, a yayin da wadanda kuma suka tsaya aka yi awon gaba da su zuwa cikin dazuka.
Wani da ya tsira da ransa da ya nemi kar a bayyana sunansa ya shaidawa majiyarmu cewa lamarin ya faru ne a daidai Rijana.
"Masu garkuwa da jama'ar sun yi amfani da damar lalacewar hanyar wanda ke sanya masu ababen hawa masu zuwa da masu dawowa ke tafiya a hankali a hannu daya", inji majiyar tamu.
A lokacin da majiyarmu ta tuntubi Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige bai dauki waya ba har ya zuwa hada wannan rahoton.
No comments