Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sandan Nijeriya Bakwai A Zamfara

  Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kashe 'yan sandan Najeriya bakwai a Jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar...

 


Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kashe 'yan sandan Najeriya bakwai a Jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar ranar Litinin da dare.

Lamarin kamar yadda rahotanni suka nuna ya faru ne a kan hanyar Tofa zuwa Magami da ke Gusau babban birnin jihar.

Wasu da suka gane wa idonsu abin da ya faru sun shaida wa Channels TV cewa maharan sun fafata da 'yan sandan ne kafin su kashe bakwai daga cikinsu.

Kazalika, an ƙona motar 'yan sanda ɗaya.

Wani mai magana da yawun Asibitin Yarima Bakura, Awwal Ruwandoruwa, ya tabbatar da cewa an kai gawar 'yan sandan asibitin na su.

No comments