Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

‘Yan Shi’a Sun Maka Abubakar Malami Da Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda A Kotu

Daga Ammar M. Rajab Mabiya Harkar Musulunci sun kai karar Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya (IGP) da Babban Lauyan Tarayya (A...


Daga Ammar M. Rajab

Mabiya Harkar Musulunci sun kai karar Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya (IGP) da Babban Lauyan Tarayya (AGF) bisa zargin tsare dan Harkar Musulunci din, Yahuza Haruna Masaka ba bisa ka’ida ba, watanni shida bayan kama shi. .

Sakataren Dandalin [alibai wanda aka fi sani da Academic Forum na Harkar Musulunci, Abdullahi Muhammad Musa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Abdullahi ya ce karar mai lamba FHC/ABJ/CS/807/2021 da aka shigar a ranar 3 ga watan Agusta, 2021, tana gaban mai shari’a Obiora Egwuatu na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

“Abin mamaki da rashin sanin yakamata, rundunar ‘yan sandan Abuja (FCT) ta yi awon gaba da wani mai muzaharar Free-Zakzaky mai suna Yahuza Haruna Masaka zuwa wani wurin da ba a sani ba wanda ake tsare da shi tun daga ranar Juma’ar 7 ga watan Mayun 2021 da misalin karfe 1430 na rana.

“Bayan wata shida, ba a ji duriyar mai muzaharar ba wanda aka yi garkuwa da shi, kuma ba a bai wa iyalansa damar isa gare shi ba har zuwa yau. Wannan rashin sanin yakamata ne na ‘yan sanda wanda ya dace ya ja hankalin al’umma,” inji shi.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, Abdullahi Musa ya ce Yahuza Haruna ya isa Wuse, Zone 3, domin ya bai wa kanwarsa (Rahma Salihu) kudin mota.

“Da isowarsa sai ya ganta a cikin wata motar Toyota Coaster sai ya matsa kusa da ita domin ya yi mata magana. Ba tare da ya sani ba, motar bas din tare da mutanen da ke cikin motar ashe ‘yan sanda ne suka kama su. Yayin da suka hango shi yana magana da ‘yar’uwarsa mace, sai ‘yan sandan suka rufe shi da duka da sanduna da muggan makamai” ya labarta.

"Bas din, tare da mutane 62 da aka riga aka kama su, an dauke su aka kai su zuwa dandalin Eagle Square," in ji shi.

A cewarsa, a lokacin ne aka mika Yahuza ga tawagar ‘yan sintiri a cikin mota kirar Hilux.

“A dandalin Eagle Square, ‘yan sanda sun gana musu azaba ta hanyar da ba ta dace ba, har ma da amfani da wutar lantarki wanda ya yi sanadin mutuwar Naziru Mu’azu daga karamar hukumar Isa ta Jihar Sakkwato ba zato ba tsammani; kuma mutane 44 sun sami munanan raunuka daban-daban”, ya tabbatar.

Ya ci gaba da labarta cewa; “shin zanga-zangar farar hula da jerin gwanon addini ba wani bangare ne na hakkokin ‘yan kasa ba?”, ya tambaya.

Abdullahi ya ci gaba da cewa; “Ta hanyar da ba ta dace da ka’idojin aikin ‘yan sanda da wadanda ke aikin ba, sun kama masu karancin shekaru (maza da mata) da masu wucewa ma ta gefen titi da ba su ma cikin masu muzaharar.

Ya kara da cewa "'yan sanda da take hakkin 'yan kasa abu ne da bai dace ba kuma abin kunya ne."

Musa ya ce ko da yake kanwar Yahuza, Rahma Salihu, an kai ta sashen ‘Anti-Vice Unit’ na ’yan sanda da ke Wuse Zone 2, amma a ranar ne aka sake ta.

“Tsawon watanni 6 da suka gabata, duk kokarin gano inda Yahuza Haruna yake abin ya ci tura. Garkuwar da jama’a na kara kamari a wannan yanki ta duniyar ta mu, abin bakin ciki ne a ce ‘yan sanda ne ke wannan halin. Ina ka’idojin aiki da ta da’a? Ko kuwa, jami'an 'yan sandan sun nutse ne cikin wani bangare na aikata abin da aka dauke su aiki a kai su yaka?” Ya tambaya.

A cewarsa, sakamakon rashin da’a da mutuntaka daga rundunar ‘yan sandan FCT a kan lamarin, ya sanya suka shigar da kara gaban babbar kotun tarayya bisa take hakki da Sufeto-Janar na ‘yan sanda da kuma babban mai shari’a na tarayya suka yi a ranar 3 ga watan Agusta, 2021.

“Lambar karar ita ce FHC/ABJ/CS/807/2021 kuma karar tana gaban Honorabul Justice Obiora A. Egwuatu.

“A yayin da muke jiran gabatar da shari’ar, muna Allah wadai da sace Yahuza Haruna da ‘yan sandan babban birnin tarayya suka yi ba bisa ka’ida ba, tare da neman a gaggauta sakin sa ba tare da wani sharadi ba,” inji shi.

No comments