Akwai yiwuwar a sake tafiya yajin aiki bayan da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i, ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin m...
Akwai yiwuwar a sake tafiya yajin aiki bayan da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i, ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin makonni uku a yau Litinin da ta cika alƙawuran da ta ɗauka.
Wannan na zuwa ne bayan da Ƙungiyar Manyan Ma'aikata na Jami'o'i da kuma ta Ma'aikatan da ba samu koyarwa ba na jami'o'i su ka gana a yau domin ɗaukar mataki na gaba a kan rashin cika alƙawuran da gwamnatin tarayya ta yi a kan buƙatunsu.
A bara ne dai Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu a kan yarjejeniyar biyan haƙƙoƙin ƙungiyoyin.
Da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja, shugaban ASUU ɗin na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya nuna rashin jin daɗinsa a bisa yadda gwamnati ta ƙi cika musu alƙawuran da ta ɗaukar musu.
"Mun baiwa gwamnatin tarayya wa'adin makonni uku. Idan makonni ukun su ka cika ba a biya mana buƙatun mu ba, to ba makawa za mu tafi yajin aiki.
"Ai mun yi ƙoƙari da mu ka basu isasshen lokaci amma har yanzu shiru," in ji shi.
No comments