Fitaccen mawakin nan É—an yankin kudu Davido ya sadaukar da kudin da masoyan sa suka tara masa har Naira miliyan 200 ya kara nair...
Fitaccen mawakin nan É—an yankin kudu Davido ya sadaukar da kudin da masoyan sa suka tara masa har Naira miliyan 200 ya kara naira Miliyan 50 a kai inda zai bada kudin har miliyan 250 zuwa ga gidauniyoyin marayu.
Mawakin ya bayyana hakan ne a shafinsa na Sada Zumunta a yau Asabar 20 ga watan Nuwamban 2021.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram da Facebook cewa; bayan da ya karbi naira miliyan 200 daga abokansa da masoyansa, domin su taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa ya yanke shawarar zai ƙara Naira miliyan 50 daga cikin kudaden shi da kuɗin ya zama Naira naira miliyan 250.
Tauraron mawakin ya kafa kwamitin mutum 5 da za su dauki nauyin raba kudaden ga gidauniyoyi daban-daban da gidajen marasa galihu fadin Nijeriya.
Takardar sanarwar;
No comments