Daga Ammar M. Rajab Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin a maido da sadarwa a a wuraren da aka datse sadarwar a sassan Kaduna. S...
Daga Ammar M. Rajab
Gwamnatin jihar Kaduna ta bada
umurnin a maido da sadarwa a a wuraren da aka datse sadarwar a sassan Kaduna.
Samuel Aruwan, Kwamishinan lura da
tsaron cikin gida shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a babbar
Sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Kaduna a yau Juma’a 26 ga watan
Nuwamban 2021.
Samuel Aruwan ya ce gwamnatin jihar
ta bai wa dukkanin hukumomin da yakamata umurnin dawo da sadarwar a inda aka
datse a wadansu kananan hukumomin jihar.
A watan Oktoban 2021 ne, gwamnatin
jihar ta datse sadarwar bisa shawarwarin hukumomin tsaro kan matakan da suka
dauka na dakile ayyukan ‘yan bindiga da ‘yan fashin daji da sauran ayyukan bata
gari a jihar. Inda Samuel Aruwan ya ce a yanzu hukumomin tsaron sun bayyanawa
gwamnatin jihar cewa suna iya maido da sadarwar.
Sai dai Samuel Aruwan ya ce datse
sadarwar da suka yi ya taimakawa hukumomin tsaro wajen samun wadansu nasarorin,
wanda hukumomin tsaron za su bayyana a kwanan nan.
Samuel Aruwan ya ce tsawaita
datsewar sadarwar zai shafi ayyuka da kasuwanci da dama na ‘yan jihar masu bin
doka da oda.
Inda ya bada tabbacin cewa za a dawo
da sadarwar daga yanzu zuwa ‘yan kwanaki masu zuwa. A yayin da masu sadarwar ke
kokarin dawo da sadarwar kamar yadda aka umurce su.
Gwamnatin ta jinjinawa ‘yan jihar
musamman wadanda datsewar sadarwar ya shafa bisa hakuri da sadaukarwar da suka
nuna.
Sai dai ya ce har yanzu dokar hana
sayar da man fetur a jarka, da na hana hawa babur, da haramta cin kasuwanni na
mako-mako da safarar shanu na nan a wadannan kananan hukumomi da aka ayyana.
No comments