Daga Muhammad Farouk Gwamnatin Tarayya da kungiyar Malaman Jami’o’i sun cimma matsaya bayan da Kakakin majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamil...
Daga Muhammad Farouk
Gwamnatin
Tarayya da kungiyar Malaman Jami’o’i sun cimma matsaya bayan da Kakakin
majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya shiga tsakani kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta labarto.
An cimma
matsayar ne a wani zaman sulhu da aka yi a majalisar kasa a Abuja a yau
Alhamis.
Kakakin
majalisar ya gayyaci ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, minister kudi, Zainab
Ahmed, da kuma jagororin ASUU din domin zaman sulhu don dakile tafiya yajin
aikin.
A yayin
zaman, an yi bitar yarjejeniyar da gwamnatin Tarayya ta cimma da ASUU din tun
2009.
A jawabinsa,
Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya ce majalisar ba za ta zura ido abubuwa
na tabarbarewa ba tsakanin ASUU da gwamnatin Tarayya. Ya ce; ‘yan Nijeriya ba
za su sake iya jurewa wani sabon yajin aikin ba, sannan kuma bai kamata ASUU su
ci gaba da amfani da yajin aiki a duk lokacin da suke so a biya bukatunsu ba.
Ya ce;
dole ne bangarorin biyu a jingina musu laifin kasa shawo matsalar da ya ki ci
ya ki cinyewa. Sai dai ya ce tabbas ASUU ta yi hakuri da gwamnati sosai, a don
haka akwai bukatar gwamnati ta girmama yarjejeniyar da suka yi.
A na
shi martanin, shugaban ASUU, Farfesa Victor Emmanuel, ya ce akwai batutuwa da
yawa da yarjejeniya da gwamnati ta yi alkawari, amma a cewarsa abin takaici ne
na yadda gwamnatin ta ki cika alkawuran da ta yi da ya hada da alawus, kayayyakin
more rayuwa, amfani da UTASS a maimakon IPPIS da sauran su wanda ya ce sune
abin da ke sanya kungiyar tafiya yajin aiki.
Ya
ce sun cimma yarjejeniya da gwamnati ta Naira Tiriliyan 1.3 za a bai wa
kungiyarsu wanda za a yi amfani da kudaden wajen bunkasa kayayyakin karatu da
sauran abubuwan dake da bukatar kudi. A cewarsa, sun amince za a biya kudaden
daki-daki, inda za a far aba su naira biliyan 200 wanda ya ce ba a biya ba har
yanzu.
Ya ce
kudin ma daga bayan an dawo da shi naira biliyan 52.127 inda Naira biliyan 30
na kayayyakin more rayuwa da kuma naira
biliyan 22.127 na alawus na Malamai, wanda ya ce ba ko daya da gwamnati ta
biya.
A na
shi jawabin, ministan ilimi, Henry Nwajuba, ya ce dukkanin abubuwan da ASUU ta
fada gaskiya ne, kuma gwamnati ta fara daukar matakin biyan bukatun nan
musamman batun alawus da kuma kudaden more rayuwa.
Ita ma
ministar kudi, Zainab Ahmed ta ce akwai batun biyan, kuma ma a yanzu haka akwai
wadansu kudaden a kasa wanda a cewarta za su biya a cikin mako.
Bayan
ministocin biyu sun kammala bayani, jagororin ASUU sun amince da sabon
alkawarin, inda suka ce za su bibiya har zuwa wa’adin da suka diba ta tafiya
yajin aiki.
No comments