YANZU-YANZU: Manchester United Ta Kori Kocinta Ole Solskjaer


Fitaccen dan jaridarnan a bangaren wallafa labaran wasanni, Fabrizio Romano ya wallafa da safiyar yau Lahadi cewa matakin korar Kocin Manchester United Ole Gunner Solksjaer da hukumar kungiyar ta dauka ya samu sahhalewar shugaban kungiyar gudanarwa Glazer. 

Yanzu haka idan ba a samu wanda zai ja ragamar kungiyar ba, Fletcher da Carrick ne za su ja ragamar kungiyar kafin kungiyar ta kai ga samun mafita. 

Post a Comment

0 Comments