YANZU-YANZU: Oobi Cubana Ya Rufe Kulob Din Abuja Saboda Mutuwar Wata Mace A CikiAttajirin dan kasuwa, Obinna Iyiegbu, wanda aka fi sani da Obi Cubana ya rufe kulob dinsa na ‘Hustle and Bustle’ da ke Abuja.

Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

An rufe kulob din ne biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru da wata ‘yar wasan kulob din wadda wutar lantarki ya kashe a daren jiya.

A cikin sanarwar, Kamfanin Cubana ya rubuta cewa: “mun rufe wurin har zuwa sabuwar sanarwa. Wannan ya faru ne sakamakon rashin abokiyar ciniki mai girma.

"Muna matukar bakin ciki da wannan lamarin kuma muna bukatar lokaci domin farfadowa daga lamarin. Addu'ar mu tana tare da iyalan ruhin da ya rasu.

“Ina tausayawa dangi kan rashin da aka yi wanda yake da wahalar jure wa. Ku yi hakuri da mu a yayin da muke fuskantar wannan babban rashin."

Post a Comment

0 Comments