YANZU-YANZU: Ƴan Sanda, DSS Sun Mamaye Hedikwatar APC A Abuja


Daga Muhammad Farouk

Rahotanni dake shigowa a halin yanzu na nuni da cewa dakarun ƴan sanda a motoci huɗu ɗauke da makamai sun tsare harabar Hedikwatar Sakatariyar APC da ke a Blantyre Street a birnin Tarayya Abuja.

Jaridar Punch ta labarto cewa a yau ne a ka kai ƴan sandan inda jami'an DSS ke mara musu baya, suka dira a harabar Hedikwatar domin daƙile yunƙurin zanga-zanga wacce fusatattun ƴan jam'iya ke shirin yi sakamakon zaɓukan shugabannin mazaɓa, ƙananan hukumomi da na jihohi.

Post a Comment

0 Comments