Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: Shugaban Kamfanin Tuwita Jack Dorsey Ya Yi Murabus

Shugaban kamfanin Tuwita Jack Dorsey ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, inda wani babban jami'in kamfanin Parag Agrawal...


Shugaban kamfanin Tuwita Jack Dorsey ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, inda wani babban jami'in kamfanin Parag Agrawal ne zai maye gurbin Mista Jack.

Mista Dorsey, wanda ya kirkiri shafin na sada zumunta a shekarar 2006, shi ke jan ragamar Tuwita tun daga wancan lokacin.

A wata sanarwa da ya fitar, Jack ya ce "lokaci ya yi da ya kamata na kauce," tare da cewa kamfanin zai ci gaba da gudana.

Ya kara da cewa ya amince da kwarewar wanda zai maye gurbinsa a matsayin shugaba, tare da mika sakon godiya gare shi, ya kuma karkare da cewa ''Lokaci ya yi da zai jagoranci kamfanin.''

A shekarar 2011 ne Mista Agrawal ya fara aiki da Tuwita, kuma tun shekarar 2017 ya ke jagorantar fannin fasahar kamfanin.

Mista Dorsey dai ya dade ya na fuskantar matsin lamba, daga masu zuba jari kan ya sauka daga mukaminsa kamar yadda BBC ta labarta.

No comments