Labarin dake shigo wa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa wadansu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari yanzu haka ...
Labarin dake shigo wa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa wadansu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari yanzu haka a gidan gyaran hali dake Jos a jihar Filato.
Majiyarmu ta ce ana jiyo karar harbe-harbe ta ko'ina.
Gidan yari wanda yanzu aka sauya masa suna zuwa gidan gyaran hali yana kusa da Hedikwatar 'yan sanda ne ta jihar Filato da kuma Hedikwatar jami'an tsaron DSS ta jihar.
Ya zuwa hada rahoton nan babu wani cikakken bayani dangane da harin.
Cikakken bayani zai zo daga baya.
No comments