Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Yawan Haihuwa Barkatai Na Hana Mu Ci Gaba A Jamhuriyyar Nijar - Gwamnati

A jamhuriyar Nijar, yanzu haka Sarakunan gargajiya daga sassan kasar na halartar wani taro domin tattaunawa kan yadda za a rage ...


A jamhuriyar Nijar, yanzu haka Sarakunan gargajiya daga sassan kasar na halartar wani taro domin tattaunawa kan yadda za a rage yawan haihuwa a kasar, wanda gwamnati ke cewa shi ne babban dalilin da ke hana wa Nijar samun ci gaba kamar yadda Gidan Rediyon Faransa na RFI ta labarto.

Shugaba Mohamed Bazoum ne ya jagoranci taron, inda ya jaddada matsayin gwamnatinsa na ganin cewa mata sun rage haihuwa a kasar.

“Wannan taro, ina da kyakkyawan fatan cewa zai taimaka wa mata wajen daidaita rayuwarsu tare da amfanin ‘ya’yan da za su haifa da kuma makomarsu”, inji shugaba Bazoum.

Shugaban ya kara da cewa, "kamar yadda na taba fada a can baya, matukar muna haihuwar ‘yaya barkatai, to lalle za mu gaza daukar dawainiyar ilmantar da su, idan har muka gaza ilmantar da su kuwa, to a na su bangaren za su haifi ‘ya’yan da za su kasance dalilin gaza habbaka tattalin arziki ballantana samar wa kanmu ci gaba."

Alkaluma sun tabbatar da cewa matukar ‘ya’ya mata suka samu ilimi na akalla karamar Sakandare, to ko shakka babu su ne za su fi taimakawa wajen samar da ci gaba a cewar shugaban na Nijar.

"A game da batun ilmantar da ‘yan mata da kuma tabbatar da cewa sun kammala karamar Sakandare, wannan ya sa gwamnati da taimakon abokan huldarta za ta gina makarantu da kuma daukar dawainiyyar ilimin ‘ya’ya mata, muna fatan yin hakan ba tare da bata lokaci ba" inji shugaba Bazoum.

No comments