Gwamnan jihar Zamfara, Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya tabbatar da cewa daga yau zuwa ranar Litinin za a bude sanarwa a ...
Gwamnan jihar Zamfara, Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya tabbatar da cewa daga yau zuwa ranar Litinin za a bude sanarwa a dukkanin kafatanin sauran kananan Hukumomin jihar tare da sauran kasuwanni da aka kulle domin kowa ya ci gaba da walwalarsa.
Idan ba ku manta ba, a ranar 4 ga watan Satumban 2021 ne dai aka toshe hanyoyin sadarwa a wasu sassa na jihar a kokarin da ake yi na yaki da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran ’yan ta’addan da suka addabi Jihar.
Sai dai a watan da ya gabata, aka dawo da hanyoyin sadarwar a Gusau, babban birnin Jihar.
Da yake jawabi ranar Asabar, jim kadan da kammala zaben shugabannin jam’iyyar APC a matakin Jihar, Gwamna Matawalle ya ce za a dawo da hanyoyin sadarwar tare da dage haramcin cin kasuwannin mako-mako a Jihar.
A cewarsa, “Daga bayanan da muka samu, an samu ci gaba matuka wajen yaki da ayyukan ’yan ta’adda a Jiharmu. Saboda haka, nan da ranar Litinin ko Talata, mutanen wadannan yankunan za su samu damar yin mu’amala da ’yan uwansu ta waya.
Gwamnan ya ce; "muna daukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa mun hana wadannan ’yan ta’addan sakat. Saboda in muna shan wahala, su ma suna sha. Dukkan wani mawuyacin halin da mutanenmu suka shiga sakamakon wannan matakin ya kusa zama tarihi,”.
No comments