Daga Wakilinmu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan mutum 15 da aka kashe a jihar Sakkwato a ranekun Lahadi da Li...
Daga Wakilinmu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan mutum 15 da aka kashe a jihar Sakkwato a ranekun Lahadi da Litinin inda ya ja kunnen 'yan bindigar cewa tabbas zai yi maganinsu baki daya.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar ya fitar, inda ya ce Shugaban kasar ya ce "wannan mummunar aika-aika ta kisan gilla da aka yi wa mutanen da ba su ji ba su gani ba ba za ta tafi a banza ba, don haka maharan za su dan-dana kudarsu."
An kai jerin hare-haren ne a yankunan kananan hukumomin Goronyo da Illela mai makwabtaka da Jamhuriyar Nijar.
Kafin harin na farkon mako, 'yan bindigar sun kai wani harin a kasuwar Goronyo cikin watan Oktoba, inda suka kashe mutum 49 suna tsakiyar cin kasuwa.
Jihar Sakkwato na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya da 'yan bindiga suka addaba, duk da ikirarin da hukumomi ke yi na cewa suna cin galaba kan su.
No comments