Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Za Mu Kawar Da Akidar Tsattsauran Ra'ayi -Gwamnatin Buhari

Nijeriya da Masar na shirin yadda za su hada hannu domin ganin sun kawar da aƙidar tsattsauran ra'ayi ko kuma ra'ayin ri...



Nijeriya da Masar na shirin yadda za su hada hannu domin ganin sun kawar da aƙidar tsattsauran ra'ayi ko kuma ra'ayin rikau.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya labarto cewa, Nijeriya dai na ta fadi tashin yadda za ta shawo kan matsalar ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini da ake fama da shi sama da shekara 10. 

Boko Haram ta fara ne a Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda take kai hare-harenta na cikin gida da waje kuma suna da alaka da kungiyoyin da ke yankin Sahel.

An ta kokarin gano meke janyo karuwar wannan matsala a kasar a kusan duka matakan gwamnati.

Jami'ar Masar ta Al-Azhar ta dade tana aiki da Nijeriya wajen gudanar da wa'azi kan juriya da hakuri da juna da kuma kyakkyawar fahimta tsakanin mutane da kuma addinai kamar yadda BBC ta labarto. 

No comments