Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Za Mu Tsai Da Ƙasar Nan Cak Idan A Ka Cire Tallafin Mai -NANS Ta Gargaɗi Buhari

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS ta ce za ta tsayar da ƙasar nan cak idan har gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur kamar y...Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS ta ce za ta tsayar da ƙasar nan cak idan har gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur kamar yadda Daily Nigerian ta labarto. 

Shugaban NANS ɗin na ƙasa, Sunday Asefon ne ya yi wannan gargaɗin a taron manema labarai a jiya Juma'a a Abuja.

Asefon ya ce ba wai ƙungiyar na adawa da cire tallafin man fetur ba ne, amma ya kamata a baiyana sharuɗɗan da a ka gindaya wajen aiwatar da cire tallafin ne ya kamata a ce an san su.

"Ba a baiyana ko ɗaya da ga waɗannan sharuɗɗan ba. Saboda haka kada ma gwamnatin tarayya ta yi tunanin cire tallafi a halin yanzu.

"Matatan man fetur ɗin mu guda huɗu dukkan su ba sa aiki. Idan ma su na aikin to aikin na su bai taka kara ya karya ba.

"Sannan ba a tuntuɓi masu ruwa da tsaki ba da za su yi duba a kan abubuwan da za su sa a cire ko kada a cire tallafin ba.

"Har yanzu fa ba a tattauna a kan makomar ma'aikatan gwamnati da iyalansu ba, amma an saka ranar aiwatar da wani abu da zai iya shafar rayuwarsu.

"Ga farashin kayaiyaki ya yi tashin gwauron zabi. Idan a ka kara kuɗin man fetur, to ba mu san ya za mu kira tashin farashin kayaiyakin da za a fuskanta ba.

"A gaskiya NANS ta kaɗu da jawabin Shugaban Kamfanin mai na ƙasa, Mele Kyari da ya ke cewa man fetur zai iya kaiwa har N340 a baɗi.

"Ƴan Nijeriya na cikin baƙin talauci, jama'a su na mutuwa ba a sani ba. Muna ta kuka a zuƙatan mu. To gaskiya idan a ka ƙara mana wata wahalar a kan wannan wacce mu ke sha, to a gaskiya za a ga fushin mu," in ji shi.

No comments