Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Zabe Bai Kammala Ba A Anambra, Da Saura, Inji INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta dakatar da sanar da sakamakon zaben gwamna da aka yi a jihar Anambra, saboda rashin y...



Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta dakatar da sanar da sakamakon zaben gwamna da aka yi a jihar Anambra, saboda rashin yin zaben a karamar hukuma daya saboda dalilai na tsaro.

Tun da fari an tafi hutun minti 30 kafin a ci gaba da sanar da sakamakon zaben, amma daga bisani mai bayyana sakamakon zaben Farfesa Florence Obi ta sanar da cewa an karbi sakamakon kananan hukumomi 20 cikin 21 da ake da su a jihar, ba kuma za a ci gaba ba sai an kammala na karamar hukuma daya.

Mai Magana da yawun hukumar Hajiya Zainab Aminu ta shaida wa BBC cewa matsalar tsaro ta janyo ba a yi zabe a karamar hukumar Ihiala ba.

''Hukumar zabe ta samu damar tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 20 cikin 21 da ake da su a jihar Anambra.

Kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasa da na dokokin zabe, to dole a bai wa duk dan Najeriya da ya kai shekaru da cika ka'idojin zabe damar kada kuri'a don haka muka ga dacewar a bai wa mutane damar kada kuri'a a wannan karamar hukuma guda daya wato Ihiala mai runfunan zabe 326, domin su yi zaben nan.

An kuma sanya ranar Talata 9 ga watan Nuwambar shekarar nan a matsayin ranar da za a gudanar da wannan zabe, kafin daga bisani a tattara sakamakon da kuma sanar da dan takarar da ya yi nasara a zaben gwamna na jihar Anambra,'' in ji hajiya Zainab.

Hajiya Zainab ta kara da cewa matsalolin tsaro da aka samu a wannan karamar hukumar su suka janyo rashin gudanar da zabe baki daya a runfunan zaben da ake da su, amma yanzu hukumar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro, sun ba da tabbatacin kara matakan tsaro domin ganin an yi zaben cikin lumana.

Tun da fari wasu rahotanni sun ce an dakatar da sanar da sakamakon zaben baki daya, saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.

Amma Hajiya Zainab ta ce babu wata matsala da aka samu, an dai tafi hutun minti 30 ne kamar yadda aka saba kafin a dawo a ci gaba da sanar da sakamakon, to sai kuma batun rashin sakamakon karamar hukuma daya ya taso da dole a dakata har sai an samu cikakken sakamakon kananan hukumomi 21 kafin hukumar zabe INEC ta ci gaba da sanar da sakamakon da ayyana dan takarar da ya yi nasara.

Sai dai duk da cewa hukumar zaben ta samu sakamakon zaben kananan hukumomi 20 daga cikin 21, mai magana d yawun hukumar ta ki ta ce uffan game da dan takarar da ke kan gaba a sakamakon da yake hannu zuwa yanzu.

-Rahoton BBC

No comments