Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Zaben 2023: Kada Ku Zabi PDP -El-Rufai Ya Roki Jama'ar Kaduna

  ......... Ku Amince Da Zabin Da Zan Yi Muku A Zaben 2023 A Kaduna –El-Rufai Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya roki al’ummar jihar K...

 


......... Ku Amince Da Zabin Da Zan Yi Muku A Zaben 2023 A Kaduna –El-Rufai


Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya roki al’ummar jihar Kaduna da ka da su zabi jam’iyyar PDP a zaben da za a yi a shekarar 2023 mai zuwa.

El-Rufai ya ce idan suka zabi PDP to za su mayar da Nijeriya cikin matsalolin da suka wuce.

Ya ce ya kamata jama’a su yi gangami su zabi wanda zai nada a matsayin Gwamnan Jihar a 2023. Gwamnan ya shawarci al’ummar Kaduna da su amince da shi a zabin da zai yi musu.

Ya yi zargin cewa idan ba don halin ja-in-ja da tsohon Sanata Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi ke yi ba, da ci gaban jihar Kaduna ya zarce irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wanda a yanzu mutanen Kaduna ke ta murna a cewarsa.

Ya ware gadar Kawo ta zamani da aka kammala, ya ce bai kamata a ba shi ladar aikin shi kadai ba, har ma da ‘yan majalisar da suka tabbatar da cewa aikin ya samu goyon bayan majalisa, da kuma jama’ar jihar Kaduna da ke goyon bayan gwamnatinsa.

A cewarsa, matakin da Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi suka dauka ya kawo koma baya ga ci gaba a jihar, inda ya nuna cewa a shekarar 2023 ya kamata jama’a su yi hattara da wanda za su kada kuri’a domin kaucewa kawo wasu makiya jihar Kaduna da ya kamata a la’anta a cewarsa.

"Tsinuwar Alllah ta fada musu," El-Rufai ya yi addu'a, aka amsa da “Amin’ cikin daga murya a al’ummar dake cikin dakin motsa jiki na Ahmadu Bello Stadium' inda daruruwan jama'a suka yi dafifi domin kaddamar da sabon tsarin kudi a jihar.

No comments