Daga Wakilinmu A jiya Talata 16 ga watan Nuwamban 2021, babbar kotun Tarayya dake Sakkwato ta fara sauraren karar da 'yan...
Daga Wakilinmu
A jiya Talata 16 ga watan Nuwamban 2021, babbar kotun Tarayya dake Sakkwato ta fara sauraren karar da 'yan'uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky wadanda aka fi sani da 'yan shi'a na Sakkwato suka shigar da Babban Sufeto Janar na 'yan Sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba da kuma Kwamishinan 'yan Sandan jihar Sakkwato, Kamaldeen Kola-Okunlola kan zargin kisan gillar da aka yi wa almajiran Shaikh Zakzaky hudu a Sakkwato a yayin muzaharar Ashura ta bana.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Alhamis din 21 ga watan Oktoban shekararnan 'yan'uwa musulmin suka shigar da kara kan zargin da suke yi wa jami'an 'yan sanda kan bude musu wuta da suka yi a ranar Alhamis 19 ga watan Agustan shekarar nan da muke ciki a daidai lokacin da suke gabatar da muzaharar Ashura a Sakkwato, wanda a cewarsu ya yi sanadiyyar kashe mutane hudu inda da dama suka sami raunuka.
A zaman kotun na jiya, Lauyoyi daga kowanne bangare sun hallara, inda bayan karanto karar, Alkalin babbar Kotun ya tambayi lauyan da yake wakiltar 'yan'uwa musulmi akan ko sun shirya a ci gaba da shari'ar? Inda Lauyan ya tabbatar da cewa a shirye suke.
Sai dai lauyan da ke kare wanda ake kara ya bayyana cewa su ba su shirya ba kasantuwar a shekaranjiya ne aka ba shi takardar shigar da karar.
A sakamakon hakan kotun ta dage zaman har zuwa ranar Talatar 23 ga watan nan da muke ciki domin ci gaba da shari'ar.
No comments