Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

‘Zidane Ya Nuna Cewa Ba Shi Da Sha'awar Horar Da Man Utd'

  Yunƙurin Manchester United na ɗauko Zinedine Zidane ya gamu da cikas, inda wasu majiyoyi na kusa da tsohon kocin Real Madrid suka ce ya nu...

 


Yunƙurin Manchester United na ɗauko Zinedine Zidane ya gamu da cikas, inda wasu majiyoyi na kusa da tsohon kocin Real Madrid suka ce ya nuna ba ya sha'awar zuwa Old Trafford.

A ranar Asabar Manchester United ta raba gari da Ole Gunner Soskjear bayan kashin da ƙungiyar ta sha hannun Watford 4-1.

A watan Mayun bana Zidane ya bar Real Madrid a matsayin kocinta karo na biyu.

Ya lashe kofin zakarun turai a Madrid sau uku a jere daga 2016.

Bayan ya bar ƙungiyar a 2018, ya sake dawo wa daga baya inda kuma ya lashe kofin La Liga da Super Cup a 2020.

Majiyoyin da ke kusa da tsohon ɗan wasan na Faransa sun ce Zidane wanda yanzu ba shi da ƙungiya ba ya da sha'awar aikin horar da Manchester United.

An alaƙanta shi da ƙungiyar Paris St-Germain ta Faransa, kuma zai fi maraba da buƙatar idan har ta samu.

Mauricio Pochettino, wanda aka fi maganarsa a matsayin wanda zai zama kocin Manchester, yanzu shi ne mai horar da PSG kuma ana tunanin Zidane zai iya maye gurbinsa.


No comments