Daga El'Zahraddeen Umar Katsina facebook sharing buttontwitter sharing buttonpinterest sharing buttonemail sharing buttonsha...
Daga El'Zahraddeen Umar Katsina
facebook sharing buttontwitter sharing buttonpinterest sharing buttonemail sharing buttonsharethis sharing button
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Tsohon Dan majalisar tarayya da ya wakilci Kananan Hukumomin Dutsinma da Kurfi a shekarar 2015 zuwa 2019 Hon. Danlami Kurfi ya yi kira ga matasan jihar Katsina musamman wadanda suka fito da yankin Dutsinma/Kurfi da su guji maimaita kuskuran da suka yi a baya.
Hon. Danlami Kurfi yana wannan magana ne ga manema labarai a lokacin bikin kaddamar da katafaran dakin taro da ke masaukin baki na ‘Hayyat Regency’ wanda kuma aka sanyawa sunan gwamna Aminu Bello Masari domin girmamawa.
Ya kuma kara da cewa zaban Kananan Hukumomi yana tafe, saboda haka ne yake son a zabi mutane hazikai wadanda za su taimaki al’umma ba wai san rai ba, ya ce kadda a zabi mutumin da zai zamewa al’umma kadangaran bakin tulo, azo ana kuka daga baya.
“Jama’a ku ke zabe ba wani ke yi maku ba, wannan yasa nake kira da ayi zaban Kananan Hukumomi cikin lumana kuma a ba jam’iyyarmu ta APC goyan baya mu ga cewa mun cinye zaban nan baki daya ko kansila daya ba zamu rasa ba in Allah ya yarda” inji shi
Hon. Danlami Kurfi ya yi gargadin cewa lallai a zabi mutanen da za su taimaki al’umma kadda ayi san rai wajan yin zaban, kadda a yarda da wanda zai yi amfani da kudi azo daga baya ana kuka kamar yadda wasu ke yi yanzu a Dutsinma da Kurfi.
A cewarsa yana fatan cewa mutanen jihar Katsina za su gyara kura-kuran da suka yi a 2019 idan kakar zaban 2023 ta zo, musamman wasu wurare yana da tabbacin za a zabi wanda zai fitar da jama’a daga kunya, wanda za surika gani, kuma idan sun buga waya ya dauka, wanda zai rika sauraransu, ba mai canza layin waya ba.
“Mu dai sama da shekara ashirin da biyar layin wayarmu daya ne kowa ya sani, ba mu tafa yinkurin canzawa ba,idan har an kira ba a samu dauka to uzuri ne, babu wani dalili da zai sa mu can layin waya, in Allah ya yarda babu abinda zai sa mu canza rayuwarmu tsakaninmu da jama’armu” inji Hon. Danlami
Daga karshe ya bada wani muhimmin sako musamman ga mutanen Dutsinma da Kurfi inda ya ce koda ba zai yi takara ba, zai cigaba da taimakon jama’arsa ta hanyar kawo mutanen kirki da za su shugabancin wannan Kananan Hukumomi guda biyu masu matukar mahimmci.
No comments