A karo na uku Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karɓi allurar rigakafin korona a fadarsa da ke Abuja a ranar Talata. A farkon wa...
A karo na uku Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karɓi allurar rigakafin korona a fadarsa da ke Abuja a ranar Talata.
A farkon watan Disamba ne hukumar lafiya a matakin farko ta Nijeriya ta ce za ta fara jaddada wa 'yan ƙasar rigakafin a karo na uku ga waɗanda suka yi a matakin farkon.
Nijeriya ta fuskanci ƙaruwar masu kamuwa da cutar ninki biyar cikin mako biyu da suka wuce, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa, inda ta ce yanzu ƙasar ta shiga zango na huɗu na annobar.
No comments