Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

A Watan Nuwamba Kawai An Kashe Ƴan Nijeriya 404- Bincike

Wani rahoto game da matsalar tsaro a Nijeriya ya ce satar mutane ta ƙaru a watan Nuwamba kaɗai a sassan Nijeriya. Rahoton ya kum...


Wani rahoto game da matsalar tsaro a Nijeriya ya ce satar mutane ta ƙaru a watan Nuwamba kaɗai a sassan Nijeriya.

Rahoton ya kuma ce an kashe mutum 404 a jihohi 28 na Nijeriya a ƙananan hukumomi 115 a cikin watan Nuwamba kaɗai.

Kamfanin Beacon Consulting duk wata yakan fitar da rahoto kan binciken da ya yi game da matsalar tsaro a Nijeriya tare da bayar da shawarwari ga mahukunta.

A cewar rahoton, satar mutane a Nijeriya ta ƙaru da kusan kashi 38 a Nuwamba idan aka kwatanta da alƙalumman rahoton na watan Oktoba.

Alƙalumman sun nuna mutum 363 aka sace a sassan Najeriya a watan Nuwamba.

Rahoton ya kuma ce an samu raguwar yawan mutanen da aka kashe da kimanin kashi 41 a ƙasar idan aka kwatanta da rahoton watan Oktoba da kamfanin ya ce an kashe mutum 636.

Rahoton watan Oktoba ya nuna wata huɗu a jere ana kashe sama da mutum 600 a Najeriya tun a Yuni, watan da aka fi kashe mutane a Najeriya a 2021 inda aka kashe mutum 1031.

Rahoton ya nuna yadda kamfanin ya gudanar da nazari da bincike da tattara alkalumansu a watan Nuwamba. Da kuma girman barazanar kai hare-hare a arewacin Najeriya duk da matakan da gwamnatin tarayya ke dauka da jihohi.

A cewar rahoton alƙaluman sun haɗa da yawan mutanen da aka kashe sakamakon rikicin Boko Haram, da kuma na ƴan fashin daji a arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya da ma waɗanda jami'an tsaro suka kashe a bakin aiki, da kuma su kansu jami'an tsaro da suka rasa rayukansu a fagen daga.

Akwai kuma ƙaruwar laifuka a yankin kudu maso yammacin Najeriya da yanayin zaɓe a jihar Anambra da fasa gidan yari da aka yi a jihar Filato.

Rahoton ya nuna yadda aka dawo da hare-haren ƴan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa a hanyar Abuja - Kaduna. Akwai kuma ƙaruwar rikicin da ya shafi na siyasa.

Rahoton ya nuna cewa yankin arewa maso yammaci aka fi kashewa da satar mutane fiye da sauran sassan Najeriya.

Alƙalumman rahoton sun nuna cewa an sace mutum 204 tare da kashe mutum 163 a watan Nuwamba. Alƙalumman sun nuna an samu raguwar yawan mutanen da aka kashe a yankin a watan Nuwamba idan aka kwatanta da rahoton Oktoba inda aka kashe mutum 258 a arewa maso yammaci.

A arewa maso tsakiya mutum 133 aka sace a cewar rahoton, yayin da aka kashe 37 a yankin.

A arewa maso gabashi, rahoton ya ce mutum biyar aka sace yayin da aka kashe mutum 151 a watan Nuwamba.

Rahoton ya ce bincikensa ya sa ido kan ayyukan jami'an tsaro kan yaƙar ƴan bindiga a arewa maso tsakiya da arewa maso yammaci a watan Nuwamba, kuma an kashe ƴan bindiga tare da cafke da dama.

Sai dai a cewar rahoton farmakin jami'an tsaron ya kasa hana kai hare-haren ƴan bindiga kan al'umma musamman yunƙurin ƴan bindigar da kwace iko a yankunan Neja da Sokoto da Zamfara da tursasa wa manoma biyan haraji ƙarƙashin jagorancin shugaban ƴan bindigar da ake kira Bello Turji.

Rahoton ya ce ana ci gaba gaba da gwabzawa tsakanin jami'an tsaron Najeriya da mayaƙan Boko Haram da na ISWAP a yankin arewa maso gabashi.

A cewar rahoton, hare-hare ta sama ya karya lagon mayaƙan Boko Haram da ISWAP wajen rage maso ƙarfin kai hare-hare a yankin Borno da Yobe da Adamawa.

Amma ISWAP da Boko Haram na ci gaba da zama barazana inda suke ƙoƙarin ƙwace ikon garuruwa da kuma kai hari da tare mutane musamman a yankin Borno, a cewar rahoton.

Shawarwari

Rahoton na ƙwararru ya ce akwai buƙatar a yi shirin ko ta kwana musamman kan nasarorin da jami'an tsaro ke samu wanda zai iya haifar da hare-hare na ramuwar gayya daga ƴan bindiga a yankin arewa maso tsakiya da arewa maso yammaci.

Binciken ya yi barazanar cewa hare-haren da satar mutane za su ƙaru saboda halin matsi na tattalin arziki da ake ciki a Najeriya da kuma tsadar farashin kayyaki a ƙasar.

Rahoton ya yi kira ga hukumomin ƙasar su fara yin ƙoƙarin magance rashin yardar da ta yi katutu a tsakanin 'yan ƙasar da nufin daƙile yawan kashe-kashen mutane da ake fama da shi.

An kuma bukaci hukumomi su ɓullo da matakan inganta tsarin zamantakewar da ya taɓarɓare musamman a arewacin Najeriya da kuma tabbatar da hukunci ga masu aikata laifuka a kasar.

(BBC HAUSA)

No comments