AFIMN Tehran Ta Yi Zaman Tunawa Da Kisan Kiyashin ZariyaDaga Sadik Alyolawy, Tehran

A ranar Alhamis 16 ga watan Disambar shekarar 2021, Dandalin dalibai da aka fi sani da Academic Forum na Tehran a Iran a karkashin Harkar Musulunci a Nijeriya ta gudanar da zaman tunawa da kisan kiyashin Zariya wanda ta auku a cikin watan Disambar shekarar 2015. 

Bayan an bude taro da addu'a, jikan Shahid Malam Turi ne Muhammad Al'amin ya bude taron da karatun Alkur'ani. Daga nan kuma Dakta Hussaini ya yi jawabin maraba ga mahalarta taron. 

Dakta Asma'u Shahid Mukhtar Sahabi ce aka gabatar a matsayin daya daga cikin shaidun gani da ido na kisan kiyashin da aka aukar a gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky. Daktar ta zayyano bayanai game da waki'ar tun daga lokacin da suka bar Kaduna har zuwa Gyallesu Anguwar da Shaikh Ibraheem Zakzaky din yake zaune. 


A ci gaba da bayanin da ta yi, ta zayyano yadda sojojin Nijeriya suka kai hari gidan Shaikh din, wanda ta lashe rayuka da dama ciki har da mijinta da mahaifinta da kuma daruruwan 'yan'uwa Musulmi da suka halarci wajen domin ba da kariya ga jagoran harkar musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky. 

Sayyid Imam Zadeh wanda ya taba zuwa da zama a Nijeriya shekaru 23 baya, shi ne babban mai jawabi a wajen taron. Malamin ya fara bayanin yadda rayuwarsa ta kasance a Nijeriya a wadancan shekarun din har zuwa lokacin da ya bar Nijeriyar din ya koma Iran. 

Shehin malamin din ya yaba kwarai yadda 'yan Nijeriya suka yi riko da Ahlul-Bayt kwarai da gaske, ya ba da labarin yadda wasu 'yan shi'ah suke bincike game da Ahlul-Bayt din cikin dukkannin yanayi na tsoro da barazana. Ya kuma jinjinawa iyalan shahidai tare da karfafar su da su yi hakuri kamar yadda aka san Sayyidah Zahra (A.S) da hakuri da juriya. 


Daga karshe ya yi addu'ar Allah ya yi karin matsayi ga shahidai, sannan da samun lafiya da kariya ga jagororin 'yan shi'ah musamman Shaikh Ibraheem Zakzaky.

Post a Comment

0 Comments